An bindige matar sabon zababben firaministan Lesotho

Matar sabon zababben firaministan Lesotho Tom Thabane wanda ake gaf da rantsarwa Lipolelo Thabeane ta rasa ranta sakamakon harbin ta da bindiga da aka yi.

Rahotanni sun ce, an harbe Lipolelo a daren Juma’ar nan a lokacin da ta ke shiga kauyensu mai nisan kilomita 35 daga Maseru babban birnin kasar.

Sakataren jam’iyya mai mulkin kasar Samonyela Ntsekele ya fitar da sanarwa cewa, Lipolelo na cikin motarta tana koma wa gida a lokacinda aka harbe ta, kua ta rasu a yayin da ake kan hanyar kai ta asibiti.Labarai masu alaka