Najeriya ta ce ana sace rabin kayan taimako da ake kai wa wadanda Boko Haram ta tsugunar

Gwamnatin Najeriya ta yi ikirarin cewa, ana sace sama da kaso 50 na kayan taimako da ake aika wa mutanen da rikicin ta'addancin Boko Haram ya tsugunar a kasar.

A wata sanarwa da kakakin mukaddashin shugaban kasar Laolu Akandu ya ce, an kafa kwamiti don bincike da kuma gano hanyoyin da za a kawo karshe sace kayayyakin taimakon.

Akande ya ce, sabon tsarin da aka kawo zai magance yadda ake sace kayan abinci kuma za a samar da sabbin dabaru wajen bayar da taimakon da mutane a Najeriya

Ya ce, a yanzu akwai tireloli 1000 da ke dauke da kayan abinci nau'ika daban-daban wadanda suke kan hanyar kai kayan taimako ga mabukata kuma hakan ta samu ne karkashin sabon tsarin da aka samar, wanda sabain yadda ya ke a baya na sace kaso 50 cikin 100 na kayan taimakon.

Wannan ne karo na farko da gwamnatin Najeriya ta amince da ana sace kayan taimakon abinci da ake bayar wa don kai wa mutanen da rikicin Boko Haram ya tsugunar a yankin Arewa maso-yammacin kasar.Labarai masu alaka