Ministan Lafiya na Tunisiya ya mutu yayin wani gudun bayar da taimako

Ministan Lafiya na Kasar tunisiya Salim Shakir ya yanke jiki ya fadi bayan samun bugun zuciya inda lkuma ya ce ga garinku nan.

Ministan Lafiya na Tunisiya ya mutu yayin wani gudun bayar da taimako

Ministan Lafiya na Kasar tunisiya Salim Shakir ya yanke jiki ya fadi bayan samun bugun zuciya inda lkuma ya ce ga garinku nan.

Ministan mai shekaru 56 ya fadi bayan yin gudun mita 500 inda aka kaishi asibitin sojoji kuma duk kokarin ceton ransa da aka yi ya ci tura.

Firaministan kasar Yusuf Shahid ya ce, ya yi babban rashin dan uwa kuma abokin aiki wanda ya mutu a lokacin da ya ke aikin bayar da taimako.

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka shirya wata gasar tsere don taimaka wa mutanen da suke fama da cutar daji ko kuma kansa a Turance.Labarai masu alaka