An kai hari a gidan ministan tsaron Libiya

Wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun kai hari a gidan ministan tsaron gwamnatin kasa ta Libiya Mahdi Al-Bargusi.

An kai hari a gidan ministan tsaron Libiya

Wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun kai hari a gidan ministan tsaron gwamnatin kasa ta Libiya Mahdi Al-Bargusi.

Daraktan yada labaran ministan Fathi Al-Fayturi ya ce, wasu da ba a san ko su waye ba ne suka kai hari a gidan ministan da ke yankin Janzur a yammcin Tarabulus.

Fayturi ya kara da cewa, a lokacin da aka kai hari Fayturi yana cikin gidan kuma masu tsaronsa sun fafata rikici da maharan amma ba a samu asarar rai ko jikkata ba.

 Labarai masu alaka