Sudan ta ce tana fuskantar barazana a iyakokinta da Masar da Eritriya

Gwamnatin Sudan ta sanar da cewa, kasar na fuskantar barazana ta bangaren iyakokin kasashen Masar da Eritriya.

Sudan ta ce tana fuskantar barazana a iyakokinta da Masar da Eritriya

Gwamnatin Sudan ta sanar da cewa, kasar na fuskantar barazana ta bangaren iyakokin kasashen Masar da Eritriya. 

Ministan Harkokin Wajen Sudan Ibrahim Ghandour ya shaida wa 'yan jaridu a birnin Khartoum a yayin gana wa da takwaransa na Habasha Workneh Gebeyehu cewa, Sudan ba ta magana kan batun gini da wata kasa ta ke yi, tana kawai batu ne kan barazanar da ake yi a kan iyakokinta.

Ya ce, akwai barazana a kan iyakokin gabashin kasar inda wasu 'yan adawa suke, kuma suna sauraren duk wani irin hatsari da ka iya fito wa daga bangaren.

Ministan ya kara da cewa, Rundunar Sojin Sudan ta aike da mayakanta zuwa yankin don samar da tsaro.

A Lahadin da ta gabata ne Sudan ta rufe iyakarta da Eritriya tare da tura dubunannan sojoji zuwa yankib Kassala.Labarai masu alaka