Cutar Sankarau ta yi ajalin mutane 7 a Gana

Mutane 7 ne suka mutu sakamakon kamu wa da cutar Sankarau akasar gana da ke Yammacin Afirka.

Cutar Sankarau ta yi ajalin mutane 7 a Gana

Mutane 7 ne suka mutu sakamakon kamu wa da cutar Sankarau akasar gana da ke Yammacin Afirka.

Mutane 19 ne suka kamu da cutar a yankin Yammacin Gonja inda 7 daga ciki suka ce ga garinku nan.

Daraktan Kula da Lafiya na yankin Saeed Muazu Jibreal ya bayyana cewa, wadanda suka mutun sun je asibiti a kurarren lokaci, kuma ana aiyuka shawo kan cutar.

Jibreal ya bukaci jama'ar yankin da su je asibiti da zarar sun ji suna ciwon kai ko wuya.

Ana daukar cutar Sankarau a iska kuma tana fara wa daga kwakwalwa daga nan kuma ta yadu zuwasauran sassan jikin mutum.

 Labarai masu alaka