Motar akori kura dauke da 'yan gudun hijira ta kife a Libiya

'Yan gudun hijira 22 ne sika mutu sakamakon kifewar motar akori kura falura da suke ciki a garin Bani Walid na yammacin Libiya.

Motar akori kura dauke da 'yan gudun hijira ta kife a Libiya

'Yan gudun hijira 22 ne sika mutu sakamakon kifewar motar akori kura falura da suke ciki a garin Bani Walid na yammacin Libiya.

Shugaban gundumar Bani Walid Ali Al-Nakarat ya bayyana cewa, motar na dauke da bakin haure sama da 100 kuma ta kife a kan hanyar da ke tsakanin Al-Sadad da Al-Karara.

Ya ce, wasu bakin haure 78 sun jimkata a hatsarin da ake zargin ya afku sakamakon gudun wuce sa a da direban ke yi.

Al-Nakarat ya ce, an kai wadanda suka jikkata asibiti kuma jami'an tsaro sun fara gudanar da binciken musabbabin hadarin.Labarai masu alaka