Buhari: Na fi son mu yi ban gishiri in ba ka manda da Boko Haram don kubutar da 'yan matan Dapchi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, sun fi son su tattauna da 'yan ta'addar Boko Haram don kubutar da 'yan matan Dapchi da suka yi garkuwa da su.

Buhari ya gana da ministan harkokin wajen Amurka Rex Tillerson da ya ziyarce Najeriya.

Bayan ganawar ta sirri, Fadar Shugaban Najeriya ta fitar da sanarwa inda aka bayyana cewa, Buhari da Tillerson sun tattauna kan batutuwan yaki da ta'addanci, yaki da cin hanci da rashawa, alakar tattalin arziki da demokradiyya da ke tsakanin kasashen 2.

Sanarwar ta ce, Buhari ya bayyana duniya kan cewa, sun amince don su kubutar da 'yan matan Dapchi d'yan ta'addar Boko Haram suka yi garkuwa da su lafiya.

Sanarwar ta rawaito Tillerson na yabon Buhari bisa yaki da cin hanci da rasha wa da ya ke yi inda ya kara da cewa, kudaden da aka kwace za su taimaka wajen kafa kasar tare da dora ta a turba mai kyau. 

Tillerson ya ce, duk wuya duk rintsi Amurka na tare da Najeriya. Kuma za ta ci gaba da taimaka mata wajen ganin tattalin arzikin kasar ya farfado. Haka kuma za ta taimaka wajen zaben shugaban kasa da za a yi a 2019.Labarai masu alaka