Kwarankwatsa ta fado kan wata Coci tare da kashe mutane 16 a Ruwanda

Mutane 16 ne suka mutu sakamakon fadowar Kwarankwatsa kan wata Majami'a da ke kasar Ruwanda.

Kwarankwatsa ta fado kan wata Coci tare da kashe mutane 16 a Ruwanda

Mutane 16 ne suka mutu sakamakon fadowar Kwarankwatsa kan wata Majami'a da ke kasar Ruwanda.

Gwamnan Nyaruguru Francoire Habitegeko ya bayyana wa 'yan jaridu cewa, Kwarankwatsar ta fado kan Cocin a lokacin da masu bauta suke tsaiwar Lahadi.

Habitegeko ya bayyana cewa, Kwarankwatsar ta kuma jikkata wasu mutanen 140 wadanda aka kai su asibiti don kula da su.

A gefe guda kuma, wani jami'i da ya zanta da tashar talabijin din Ruwanda ya ce, ginin Cocin ba shi da tsarin kariya daga Kwarankwatsa.

A ranar Juma'ar da ta gabata ma an samu Kwarankwatsa da ta fado wa dalibai 8 a lokacin da ake ruwan sama a garin Rusenge na Kudancin Ruwanda inda daya daga cikin daliban ya mutu.Labarai masu alaka