Buhari ya yi fatali da dokar neman sauya lokutan zaben 2019 a Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi fatali tare da kin sanya hannu kan sabuwar dokar da ke neman a sauya lokutan gudanar da zabe a kasar.

Majiyoyinmu sun raiwato cewa, shugaban ya bayar da dalilai 3 da suka sanya shi kin sanya hannu kan dokar wadda Majalisar Wakilai da ta Dattawan Kasar suka amince da ita.

Rahotanni sun ce, shugaban ya aike wa da Majalisar wannan mataki a wasu wasiku guda 2 da aka kai wa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da na Wakilai Yakubu Dogara.

Ana sa ran Shugabannin Majalisar za su karanta wasikun a zaurukansu a tsakanin ranakun Talata da Alhamis din nan.

Dokar dai na neman a sauya lokutan zabe ta yadda za a fara gudanar da zaben 'yan majalisu sannan na Shugaban Kasa.Labarai masu alaka