Hari da makami ya rutsa da rayukan mutane 25 a Filaton Najeriya

Wasu 'yan bindiga dadi sun harbe mutane 25 a kauyukan Kaura da Basa na jihar Filaton Tarayyar Najeriya, har lahira.

Hari da makami ya rutsa da rayukan mutane 25 a Filaton Najeriya

Wasu 'yan bindiga dadi sun harbe mutane 25 a kauyukan Kaura da Basa na jihar Filaton Tarayyar Najeriya, har lahira.

Kakakin 'yan sandan yankin, Mathias Tyopev ya sanar da cewa a jerin wadanda suka mutu akwai yara 3 da mata 3.

Tyopev ya kara da cewar, kawo yanzu ba a san ko su waye ba suka kai wannan harin.

Tuni aka fara bincike kan wannan lamarin.

Lokaci zuwa Lokaci jihar Filato na fuskantar kazamar fada tsakanin makiyaya da manoma.

A 'yan kwanaki 2 da suka gabata ma, ire-iren wadannan fitintinun suN yi sanadiyyar mutuwar mutane 16.Labarai masu alaka