Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 13 a Mali

Mutane 13 ne suka mutu sakamakon afkuwar ambaliyar ruwa a Mali da ke Yammacin Afirka.

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 13 a Mali

Mutane 13 ne suka mutu sakamakon afkuwar ambaliyar ruwa a Mali da ke Yammacin Afirka.

Daraktan Kare Fararen Hula Kanal Seydou Doumbia ya ce, ambaliyar ta barke a kusa da kogin Nijar inda wasu karin mutane 14 suka samu raunuka.

Doumbia ya kara da cewa, gidaje dubu 15,600 sun samu matsala a yankin.

Mahukunta sun ce, akwai yiwuwar balahirar ta ci gaba saboda ruwan saman da ake ci gaba da samu a yankin.

Daraktan Magance Annoba Yaya Boubacar sun samar da wurin fake wa na wucin gadi ga wadanda ambaliyar ta rutsa da su.Labarai masu alaka