Ana zanga-zangar adawa da cin hanci a Morokko

A garin Kasabalanca na kasar Morokko dubunnan jama'a sun gudanar da zanga-zanga tare da kira da a kawo karshen cin hanci da rashawa a kasar.

Ana zanga-zangar adawa da cin hanci a Morokko

A garin Kasabalanca na kasar Morokko dubunnan jama'a sun gudanar da zanga-zanga tare da kira da a kawo karshen cin hanci da rashawa a kasar.

Al'umar sun taru a dandalin Al-Nasr tare da kira ga Hukumar Kare Kudaden Morokko da ta yaki cin hanci da rashawa.

Mutanen sun dinga daga allunan kira da a kawo karshen cin hanci da rashawa.

Firaministan Morokko Sadeddin Al-Usmani a watan da ya gabata ya ce, sakamakon cin hanci da rashawa kasarsa ta yi asarar gina manyan asibitoci na zamani guda 50. 

 Labarai masu alaka