Ta hadu da makauniyar kyama daga Faransawa,don Musulma ce ita

Hadarin kalaman kyamar Islama da na cin zarafi da ya dinka malala kamar da bakin kwarya kan wata matashiya Musulma, ya tirsasa ta janyewa daga gasar nuna zakin murya ta “The Voice” wacce tashar talabijin kasar Faransa TF1 ta shirya.

Matashiyar mai suna Mennel Ibtissem ta ci karo da tsagwaron kyama daga Faransawa,wadanda suka yi gunduwa-gunduwa da rigar mutuncinta,duk da tuni ta fara samun fifiko daga bangaren alkalai,saboda zakin muryarta.

Ibtissem mai shekaru 22 da haifuwa,ta bayyana aniyarta ta janyewa daga gasar a shafinta na Facebook tare gode wa dukannin wadanda suka jajinta mata game wannan iftila’in da ta fada.

Matashiyar dai ta fuskanci fushin daruruwan dubban masu wariyar launin fata da na makiya Islama a shafukan sada zumunta na Facebook da Twitter,sabili da ta Musulma ma ce ita, ta furta kalaman larabci, ta daura adiko a kanta,kana daga karshe kuma ta rera wata waka mai suna “Ki yi murmushi Falasdinu” a daren Asabar na makon da ya  gabata, da zummar nuna goyon bayanta ga al’umar Falasdinu.Labarai masu alaka