An jikkata mutane 180 a yayin bikin facaka da lemon bawo a Italiya

Mutane 180 ne suka jikkata sakamakon bikin gargajiya na facaka da lemon bawo da aka yi a kusa da yankin Torino da ke arewacin Italiya.

Daruruwan mutane ne suka taru a garin Ivrea tare da hawa kekunan doki da aka cika su da lemon bawo tare da sanya tufafin irin na mutanen zamanin farko.

A rana ta farko ta bikin da zai dauki kwanaki 3 an farfasa dubunnan lemukan fata.

Mutanen da suka je kallo kuma ba sa son a yi wasan jifan juna da su sun saka jajayen huluna.

An yi imanin cewa, an fara bikin yaki da lemon bawo a zamanin farko.Labarai masu alaka