Wani gidan ajje kayan tarihi a Amurka ya kwace kambin da ya ba wa shugabar kasar Myammar

Gidan ajje kayan tarihi na Holocaust da ke Amurka ya kwace kyautar kambin da ya ba wa Shugaban kasar Myammar Aung San Suu Kyi inda ya bukace ta da ta yaki yadda ake karkashe al’umar Musulmin Rohingya.

Gidan ajje kayan tarihin ya bayyana cewa, ya dauki wannan matakine sakamakon yadda Suu Kyi ta ki daukar matakin kawo karshen kisan gila da zaluncin da ake yi wa al'umar Musulman Rohingya.

Sanarwar da gidan ajje kayan tarihin ya fitar a shafinsa na yanar gizo ta ce, manufarsu ita ce inganta zaman lafiya, kare hakkin da adam, magance kisan kare dangi danuna kyama. 

Sanarwar ta ce, an ba wa Kyi kyautar ne a shekarar 2012 bayan ta nuna kin amince wa da kama karyar sojoji, amma a yanzu kuma saboda nuna halin ko in kula ga batun Musulman Arakan ya sanya an kwace kambin.

A watan Nuwamban bara ma Majalisar Birnin Oxford na Ingila ta janye kambin da ta ba wa shugabar ta Myammar.
 
 Labarai masu alaka