Firaministar New Zealand na Naƙuda

An kwantar da Firaministar New Zealand Jacinda Ardern a asibiti sanadiyyar naƙuda.

Firaministar New Zealand na Naƙuda

An kwantar da Firaministar New Zealand Jacinda Ardern a asibiti sanadiyyar naƙuda.

Ofishin Firaministar ƙasar ta fitar da sanarwar cewa Firaminista Ardern wacce ke da juna biyu mai wata tara an kwantar da ita asibitin dake garin Auckland domin haifuwa.

Firaministar ƴar shekaru 37 da aka yi hasashen zata haifu a ranar 17 ga watan Yuni ba'a bayyana jinsi jaririnta Ba.

Idan ta sauka lafiya za ta kasance macce ta biyu da za ta haifu akan karagar mulki baya ga firaministan Pakistan Benazir Butto a duniya.

Butto a lokacin da take firaministan Pakistan ta haifi ɗiya mai suna Bakhtiyar Botto Zerdari a shekarar 1990.

 Labarai masu alaka