'Yan yawon bude ido sama da miliyan 10 ne suka ziyarci Antalya a bana

Yankin Antalya na Turkiyya na ci gaba da kafa tarihi kan harkokin yawon bude ido a bana inda ake ta shakatawa.

'Yan yawon bude ido sama da miliyan 10 ne suka ziyarci Antalya a bana

Yankin Antalya na Turkiyya na ci gaba da kafa tarihi kan harkokin yawon bude ido a bana inda ake ta shakatawa.

A wannan shekarar 'yan yawon bude ido miliyan 10 da dubu 47 da 672 ne suka shiga Antalya ta filayen tashi da saukar jiragen sama.

Idan aka kwatanta da shekarar 2017 adadin ya karo da kaso 25 in aka kwatanta da 2016 kuma ya karu da kaso 110. Adadin na bana ya karu sama da na 2014 da mutane dubu 621.

A wannan shekarar ana sa ran Turkiyya za samu kudaden shiga har dala biliyan 35 daga harkokin yawon bude ido inda ake kuma sa ran mutane sama da miliyan 35 ne za su ziyarci kasar.Labarai masu alaka