Za a nuna shirin fim na harshen Larabci na farko a gidajen Sinima da aka bude a Saudiyya

A ranar Alhamis din nan za a nuna shirin fim na farko na harshen Larabci a Saudiyya wanda wannan ne karo na farko da za a yi hakan tun bayan dawo da gidajen Sinima a kasar.

Sunan fim din "Bedle" na da dan wasan dan kasar Masar mawaki Tamir Husni a matsayin jarumin cikinsa, kuma a sanarwar da ya fitar ta shafinsa na sada zumunta na yanar gizo ya ce, daga ranar 20 ga watan Satumba za a fara nuna shirin a gidajen Sinima na Saudiyya.

A mako na 3 na watan Agusta aka nuna shirin a Masar da wasu Kasashen Larabawa wanda wannan ne karo na farko da za a nuna shi a Saudiyya kuma shi ne shirin Larabci na farko da za a nuna a kasar.

Za a nuna shirin a gidajen Sinima da ke Riyadh Babban Birnin Saudiyya.Labarai masu alaka