An kai wai Musulmi harin ta'addanci a Ingila

Wani dan ta'adda da ke tuka motar akori-kura ya bi ta kan Musulmai da ke Sallar Tarawih a filin shakatawa na Finsbury da ke Landan babban birnin kasar Ingila.

Mutane 10 ne suka jikkata sakamakon harin inda 3 daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali.

Limamin Masallacin Finsbury ya ce, an samuw adanda suka mutu sakamakon harin da aka kai wa Musulmai.

An kama mutum 1 sakamakon lamarin inda wasu mutane 2 suka gudu kafin a kama su.

Ba a bayyana ko waye mutumin da aka kama din ba.

Firaministar Birtaniya Theresa May ta bayyana cewa, wannan hari ne mummuna kuma na ta'addanci.

Shugaban Majalisar Musulmin Birtaniya ya bayyana harin a matsayin na ta'addanci da aka nufi Musulmai.

Shaidun gani da ido sun kuma ce, maharin ya yi ihu tare da cewa, "Zan kashe Musulmai" ,nda ya kutsa kai kansu da motar tasa.Labarai masu alaka