Mutane 100 sum mutu sakamakon barkewar cutar Kolera a Yemen

Kamar yadda Kungiyar Lafiya ta Duniya ta bayyana sakamakon barkewar cuta Kolera a Yemen Kimanin mutane 100 suka rasa rayukansu.

Mutane 100 sum mutu sakamakon barkewar cutar Kolera a Yemen

Kamar yadda Kungiyar Lafiya ta Duniya ta bayyana sakamakon barkewar cuta Kolera a Yemen Kimanin mutane 100 suka rasa rayukansu.

Kamar yadda sanarwar ta nuna baya ga babbar birnin Sana, cutar ta yadu zuwa garuruwa kamar su Hudey, Hacce inda ake hasashen kimani mutane dubu 160 na dauke da kwayar cutar koleran, inda ake ganin kusan rabbinsu yara kanana ne.

Kungiyoyin masu zaman kansu sun bayyana cewa a kowani minti yaro daya na kamuwa da cutar.

Sabili da cutar dai asubitoci sun cika makil

An kuma bayyana cewa rashin samun tsabtattacen ruwan shane ke haifad da cutar

A sabili da rikicin shekaru 2 a kasar ta Yemen dai yasa ba'a samun ruwan sha mai tsabta, hakan yasa kusan mutane milyan 3 basa samu ingattaccen ruwan sha , hakan ya haifad da bunkasr yaduwar cutar ta kolera

 Labarai masu alaka