UNICEF: Rikicin Yaman ya haramta wa miliyoyin yara mata zuwa makaranta

Asusun Tallafawa Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya sanar da cewa, kaso 31 cikin 100 na yara kanana mata a kasar Yaman ba sa zuwa makaranta sakamakon rikicin da ake yi a kasar.

Wakilin UNICEF a ksar ta Yaman ya fitar da sanarwa ta shafin yanar gizo cewa, al'amura a Yaman suna ci gaba da munana sakamakon ci gaba da rikicin da ake yi.

A watan da ya gabata UNICEF ta fitar da sanarwa cewa, akwai malaman makaranta dubu 166,000 da ba su karbi albashi ba tun watan Oktoban shekarar 2016, kuma akwai yara dalibai sama da miliyan 4.5 da ba sa zuwa makaranta.

Tag: Yaman , Ilimi , UNICEF

Labarai masu alaka