Wani bata-gari ya kai wa mace sanye da hijabi hari a Kanada

Wani mutum mai kyamar Musulunci ya kai wa wata yarinya mai shekaru 11 da ke sanye da hijabi mai suna Khaulah Noman farmaki a garin Toronto na Kanada inda ya yi kokarin yanka hijabin nata da almakashi.

An gano lamarin ne bayan da itayen yarinyar suka kai kara ofishin 'yan sanda.

Khaula Noman daliba a makarantar Pauline Johnson Junior ta gamu da wannan mummunan hari ne a lokacin da ta ke tafiya makaranta tare da dan uwanta Muhammd Zakariyya.

An bayyana cewa, a lokacin da ta ke tafiya ne sai ta ji alamun ana bin ta a baya wanda hakan ya sa ta waiwaya wa.

Nan da nan sai ta ga bata-garin da almakashi yana nemna yanka hijabinta.

Bayan ta gudu amma ya sake bin ta tare da ci gaba da yayyaga hijabin nata.

Firaministan Kanada Justin Trudeau ya ce, zuciyarsa na tare da wannan yarinya da aka kai wa hari.

Tuni 'yan sandan kasar suka fara gudanar da bincike.Labarai masu alaka