An kashe mutane 3 a wajen zanga-zanga a Venezuela

Mutane 3 ne suka mutu sakamakon harbin su da aka yi a wajen zanga-zangar adawa da karancin abinci a jihar Merida ta kasar Venezuela.

An kashe mutane 3 a wajen zanga-zanga a Venezuela

Mutane 3 ne suka mutu sakamakon harbin su da aka yi a wajen zanga-zangar adawa da karancin abinci a jihar Merida ta kasar Venezuela.

An kuma jikkata mutane 16 a wajen wani hargitsi da ya faru a wajen layin sayen kayan abinci.

Haka zalika an kai hari a wasu gidajen gon aguda biyu  ajihar inda mutanen da suka kai harin suka kashe shanun da ke gidan gonar.

A shekarar da ta gabata an kashe mutane 125 a zanga-zangar da aka yi a fadin kasar Venezuela saboda karancin abinci, tashin kayan masarufi da karuwar aikata muggan laifuka.

 Labarai masu alaka