Musulman Rohingya za su koma garuruwan su

Hukumomin Bangaladash da Myanmar sun aminta akan mayar da Musuluman Arakan da ke gudun hijira a Bangaladash sanadiyyar cin zalin gwamnatin Myanmar zuwa garuruwansu.

Hukumomin biyu su kai ga yarjejeniyar shirin maida Musulman Rohingya zuwa garuruwan su dake Myanmar bayan da su ka kwashe watannin su na zaman gudun hijira a kasar Bangaladesh dalilin kisar gilla da ha'incin da sojojin Myanmar da 'yan addinin Budah su ka gudanar akan su.

An bayyana cewar za'a maida su garuruwan su dake Myanmar a cikin shekaru biyu, saboda a ko wacce sati mutum 500 ne za'a karba. Za'a kididdige wadanda zasu koma da kuma dukkanin iyalen su.

Fiye da mutum dubu 740 ne dai ke gudun hijira a Bangaladesh.

 Labarai masu alaka