Bambarakwai, namiji yayi wa mata dubu 4 fintinkau a gasar kyau !

Alkalan gasar sarauniyar kyau ta kasar Kazakistan sun yi kacibus da abin ta’ajibi, a daidai lokacin da suka bayyana sunan wacce ta zama sha kalon watan sallar shekarar bana.

Bambarakwai, namiji yayi wa mata dubu 4 fintinkau a gasar kyau !

Alkalan gasar sarauniyar kyau ta kasar Kazakistan sun yi kacibus da abin ta’ajibi, a daidai lokacin da suka bayyana sunan wacce ta zama sha kalon watan sallar shekarar bana.

A Kazakistan wata matashiya mai suna Arina Aliyeva ta tura hotunanta ga kwamitin da ke ruwa da tsaki a gasar sarauniyar kyau da aka shirya a kasar a bana.

Bayan an raba dan duma da kabewa a cikin ‘yan mata dubu 4 wadanda suka halarci wannan gasar, alkalai sun yanke shawarar  bai wa Arina kambin kyau.

Amma abin mamaki, a dadai lokacin da suka kuduri aniyar ayyana sunanta,sai matashiyar ta yanke musu hanzari, tare da bayyana musu cewa, namiji ce ita ba mace ba.Abinda ya yi matukar bai wa duniya mamaki,inda a yanzu haka ake ci gaba da zazzafan cece-kuce a kafafan yada labarai da shafukan sada zumunta na duniya.

Da yake jawabi a gaban manema labarai,Arina Aliyeva wanda sunansa na ainahi shi ne Ilay Dagilev, ya ce :

“Na yanke shawarar shiga wannan gasar, sabili da wata gardama da ta hada ni da abokaina.Ni mutum mai sha’awar bunkasa kyan asali wanda yayi hannun riga da kyan kyalkyali ko kuma kwaskwarima.Za ku lura da cewa yawanci’yan matan wannan zamanin,shiga da kuma kwalliyarsu iri daya a ko da yaushe.A Ganinsu,suna birgewa,amma bana tunanin hakan”.

An fidda Dagilev daga gasar,inda aka mika kambin kyau ga wata matashiya mai bi masa.

Wannan lamarin yasa Ilay ya yi matukar farin jini a cikin wajen kasar Kazakistan.



Labarai masu alaka