Kim Jong-Un ya watsa kasa a idon Mike Pence

Kim Jong-un ya watsa kasa a idon mataimakin fraministan Amurka,Mike Pence wanda ya je Koriya ta Kudu takanas don ganawa da tawagar Koriya ta Arewa a sirrance,

Kim Jong-Un ya watsa kasa a idon Mike Pence

Kim Jong-un ya watsa kasa a idon mataimakin fraministan Amurka,Mike Pence wanda ya je Koriya ta Kudu takanas don ganawa da tawagar Koriya ta Arewa a sirrance.

A baya,Koriya ta Arewa ta amince wasu da daga cikin jiga-jiganta su gana da Pence, a daidai lokacin a ke gudanar da gasar wasanni motsa jiki na hunturu a yankin PyeongChang na Koriya ta Kudu.Amma a sa'ilin da aski ya zo gaban koshi,sai Kim Jong Un ya soke ganawar babu sani babu sabo.

Kakakin Pence, Nick Ayers ya ce Kim ya hakan sabili da sukar mataimakin firaministan Amurka ya dinka sukar Koriya ta Arewa tare da zargin ta da take hakokkin bil adama.

Ayers ya ci gaba da cewa:

"Shugabannin Koriya ta Arewa,wadanda suka dinka yin farfaganda a fagen siyasar duniya, a daidai lokacin ake gudanar da wasannin olympics, sun yi alkawarin tausasa lafuzzansu tare da bada tabbacin yiwuwar ganawarsu da Pence.Amma  mataimakin firaminstan Amurka,ya ziyarci Koriyawan da suka guje daga Arewa don neman mafaka a Kudu da kuma zuwa Pyoengchang da mahaifin wani Ba'amurke,mai suna Otto Wambier wanda ya rasa ransa, sakamakon azabar da ya sha a kurkukun Koriya ta Arewa.A shekarar 2016, Koriya ta Arewa ta yanke wa Otto hukuncin daurin shekaru 15 a gidan wakafi,sabili da zargin sa da aka yi da sace wani hoton talla,inda daga karshe aka isa da shi Amurka a sa'ilin da ya tsunduma doguwar sumar da aka kasa tantance umal'aba'isar afkuwarta".

Mai magana da yawun ministan harkokin wajen Amurka,Heather Nauert kuma, cewa yayi :

"Ziyarar da Pence ya kai Pyeongchang,ta haifar da fatan (ko da ko kankanuwa ce) ganawa da shugabannin Koriya ta Arewa,amma duk da mataimakin firaministan Amurka ya kasance a shirye,Kim Jong Un ya yanke shawarar soke ganawar.Muna bakin cikin rashin samun nasarar fa'idantuwa da wannan damar.Pence na gaf da gaya wa wakilan Koriya ta Arewa cewa,shirin nukiliyarsu haramtacciya ce,shi yasa ya ci a ce sun gaggauta yin watsi da wannan yunkurin".

Duk da hannunka mai sanda da aka dinka yi masa, Pence ya aika goron gayyata ga kanwar KimJong Un a wani taro da shugaban kasar Koriya ta Kudu ya shirya.

A lokacin wasannin share fage na olympics na bana, Mike Pence bai gaisa ba da shugaban tawagar Koriya ta Arewa da ke zaune kusa da shi a filin wasa.

 Labarai masu alaka