"Jinin Turawa bai fi na Musulman Arakan tsada ba"

Dan majalisar dokokin Burtaniya, Wajid Khan ya ce abin bakin ciki ne ganin yadda Tarayyar Turai ke ci gaba da nuna halin ko-in-kula da irin wulakanci, cin zarafi, zalunci, da kisan gillar da gwamnatin Myanmar ke yi wa Musulman Arakan.

Khan wanda ya kai ziyara sansanin masu neman mafaka na Cox Bazar da ke Bangaladesh, ya ce:

"Kashe mutum saboda ba mabiyin addinin buddah ba ne a karni na 21,abu ne mai matukar kona zuciya.Tun a lokacin da wannan matsalar ta kunno kai ya zuwa yanzu, akwai milyoyin Musulman Arakan wadanda suka nemi mafaka a Bangaladesh.A Cox, akwai marayu dubu 27 da mata masu juna-biyu dubu 60, wadanda ke ci gaba da gwagwarmaya don ci gaba da rayuwa.A lokacin da hawaye suka dinka kwarara a idanunsu, kungiyoyin agajin kasar Turkiyya ne suka fara garzayawa don agaza musu.A yanzu haka,mutanen da ake iya cutarwa a ko yaushe,matan da aka yi wa fyade da kuma konannun kauyuka ne kawai suka yi saura.Ya kamata a gagguta dauka matakai tare da gurfanar da gwamnatin Nyanmar gaban manyan laifuka don ladaftar da ita.Kamata yayi kasashen duniya su yi amfani da murya daya don yin Allah wadai da zalunci ko a ina yake a duniya.Ai jinin Turawa bai fi na musulman Arakan tsada ba.Ba wai tallafi kawai suke bukata ba,suna son a kawo karshen zaluncin da suke fama da shi".

 Labarai masu alaka