Yara kanana 4 sun mutu sakamakon zaftarewar kasa a Indonesiya

Yara kanana 4 ne suka mutu sakamakon zaftarewar kasa da ta afku a Indonesiya bayan mamakon ruwan sama da aka samu a wasu yankuna.

Yara kanana 4 sun mutu sakamakon zaftarewar kasa a Indonesiya

Yara kanana 4 ne suka mutu sakamakon zaftarewar kasa da ta afku a Indonesiya bayan mamakon ruwan sama da aka samu a wasu yankuna.

Jaridar Republica ta Indonesiya ta bayyana cewa, lamarin ya afku a yankin Purbalingga na tsakiyar Java inda baya ga yara 4 da suka mutu, wasu mutane 6 sun jikkata.

Mahukunta sun ce, za a biya diyya ga mutanen da lamarin ya shafa.

Indonesiya kasa ce mai zafi kuma na a yankin da ake yin ruwan sama kamar da bakin kwarya, kuma a kowacce shekara ana samun zaftarewar kasa sakamakon mamakon ruwan da ake samu.Labarai masu alaka