An kashe 'yan sanda 8 a wani harin bam a Indiya

'Yan sandan Indiya 8 ne suka mutu sakamakon fashewar wani bam da aka binne wanda ya tashi a lokacin da motarsu ke wuce wa.

An kashe 'yan sanda 8 a wani harin bam a Indiya

'Yan sandan Indiya 8 ne suka mutu sakamakon fashewar wani bam da aka binne wanda ya tashi a lokacin da motarsu ke wuce wa.

An binne bam din a gefen hanya a gundumar Sukma da ke jihar Chhttisgarh ta tsakiyar Kasar Indiyainda aka kuma tashe shi daga nesa a lokacin da 'yan sandan ke wuce wa da motarsu mai sulke.

Wasu 'yan sandan 10 sun samu raunkuka wadanda 4 daga cik,n suke cikin halin rai mutu kwakwai.

An kai mutanen da suka jikkata zuwa asibiti.

'Yan sanda sun ce, 'yan tawayen Maoju ne suka kai harin.

'Yan tawayen Maoju suna kwaikwayon tunanin shugaban juyin juya halin China Mao Zedong inda tun shekarar 1967 suke kai hare-hare a tsakiya da gabashin Indiya.

 Labarai masu alaka