Turkiyya ta yi wa Jamus hannunka mai sanda

Mataimakin firaminista,kana kakakin gwamnatinTurkiyya,Bekir Bozdağ ya ce sun yi wa Jamus hannunka mai sanda game da hare-haren ta'addabnci da ake kaiwa masallatan Turkawa a kasar.

Turkiyya ta yi wa Jamus hannunka mai sanda

Mataimakin firaminista,kana kakakin gwamnatinTurkiyya,Bekir Bozdağ ya ce sun yi wa Jamus hannunka mai sanda game da hare-haren ta'addabnci da ake kaiwa masallatan Turkawa a kasar.

Bozdağ ya gana da manemai labarai bayan taron majalisar ministocin Turkiyya,inda ya ce:

"Nan da wani matsakaicin zamani, sojojin Turkiyya wadanda ke ci gaba da kaddamar da hare-haren reshen zaitun tun a ranar 20 ga watan Janairu tare da yin nasarar aika 'yan ta'adda dubu 3 da 381 barzahu, za su dukufa zuwa cibiyar Afrin don tsaftace ta.Tun farkon wadannan hare-haren a yankin Afrin,sojojin Turkiyya 42 ne suka yi shahada,inda wasu 202 kuma suka jikkata.Babu wanda ya taba farar hular Siriya ko daya ba.Ganawarmu da kasar Amurka kan batun tsaftace Menbiç na Sham daga haramtattun kungiyoyin ta'adda, na ci gaba haikan.Idan an kasa cimma matsaya,Turkiyya shirye take wajen ganin bayan 'yan ta'adda.Tattaunawarmu da shugabannin Iraki kan batun yakar ta'addanci a arewacin kasarsu ta haifar da da mai ido.Kar wanda ya tambayi ni ko yaushe ne za a kaddamar hare-haren tabbatar da tsaro a Iraqi.Za mu gane wa idanunmu.Ranar da suka ga jiragenmu na yaki da sojojinmu,za su fahimci cewa mun iso".

Da ya tabo batun hare-haren ta'addanci da magoyan bayan kungiyoyin ta'adda,wadanda ke Jamus ke kaiwa masallatan Turkuwa,Bozdağ ya nuna damuwarsa,inda ya ce :

"Tabbatar da tsaro ga Turkawan Jamus, nauyi ne da ya rataya wuyan hukumomin Balin.Amma kawo yanzu ban ga wani da aka hukunta ko kuma tisa keyarsa gaban kotu ba.Tsuke bakin da gwamnatin Jamus ke ci gaba da yi, lamari ne da ya kamata a zurfafa tunani kan sa.A yu mun yi wa jakadan Jamus hannunka mai sanda".

 

 

 Labarai masu alaka