Allah daya gari bamban: An biya kyanwa tarar dala $700,000

Alkalan kotun birnin California kasar Amurka sun tirsasa wani kamfanin sarrafa lemun kwalba biyan tarar dalar Amurka $700,000 (akalla naira milyan 252) ga wani mage mai suna Grumpy,sakamakon yin amfani da hotonsa da aka yi ba bisa ka’ida ba.

A cewar  jaridar Washington Post,mai magen,misiz Tabatha Bundesen ta yankin Morristown da ke Arizona da shugabannin wani kamfanin lemun kwalba,sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar kasuwancin kofi zalla,inda za a dinka amfani da hoton magenta.Amma daga karshe kamfanin yayi amfani da wannan hoton don siyar da wasu hajojinsa na daban.Abinda yasa ta kai kara kotu.

Illahirin alkalan  da suka halarcin wannan shari'ar sun tuhumi shugabannin kamfanin lemun da yin ba-daidai ba,inda suka ce dole ne sun biyar tarar dalar Amurka 700,000 ga kyanwar, saboda an yi amfani da hotonta ba bisa ka'ida ba.

Tag: kamfani , lemu , mage , kyanwa

Labarai masu alaka