Kyaukaywar shaidar da hamshakan Kirista da Yahudawa suka yi wa Manzo

Kyaukyawar shaidar da wasu hamshakan masana Kirista da Yahudawa suka yi wa Manzon Allah (SAW)

Kyaukaywar shaidar da hamshakan Kirista da Yahudawa suka yi wa Manzo

Kyaukyawar shaidar da wasu hamshakan masana Kirista,Yahudawa suka yi wa Manzon Allah (SAW)

1-Fiodor Mikhaïlovitch Dostoïevski: Shahararren marubucin kasar Rasha,wanda aka haifa a ranar 30 ga watan Oktoban shekarar 1821 a Moscow,kana ya kwanta dama a shekarar 28 ga watan Janairu 1881 a Saint-Pétersbourg ya ce:

"Babban manzo ya keta samaniya,inda ya gana da Ubangijin al arshi.Ko shakka babu,na yi imani da Israh da Miraj har cikin raina"

2-Goethe: Babban marubuci, kwararre a fannin adabi da siyasa na kasar Jamus,wanda aka haifa 28 ga watan Agustan shekarar 1749 a Frankfurt,kana ya kwanta dama a Weimar, ya ce :

"Muhammad yayi abinda babu wani Bature da ya taba yin sa, duk da cigaban da muke da shi a fannin fasaha da kimiyya.Babu wanda ya isa ya cimma masa.Na bincika a tarihin duniya, don in gano mafificin misali ga dukannin halittun duniya, ban ga kamar Muhammad ba".

3.Alphonse de la Martine: Babban marubuci,shahararren dan siyasa kasar Faransa ,wanda aka haifa a 21 ga watan Yulin shekarar 1790 a Macon,kana ya kwanta dama a ranar 28 Fabrairu a shekarar a 1869 a Paris, ya ce :

" Idan girmar makoma,karanci kayan aiki, da kuma gagara misalin nasara za su kasance ma'aunan ilimin bil adama,wa ya isa ya kwantata kansa da Muhammad, mafificin mutun, wanda zuciyarsa ke cike makil da rahama ? Ko shakka babu ba a taba kamar sa ba, kuma ba za a taba yin kamar sa har karshen duniya".

4.Léon Nikolajeviç Tolstoï: Babban marubucin kasar Rasha,,wanda aka haifi a ranar 9 ga watan Stumban shekarar 1828 a Yasnaya Polyana,kana ya kwanta dama a Lev Tolstoy a ranar 20 ga watan Nuwamban shekarar 1910, ya ce :

"Muhammad ya fi karfin manzo, ya kasance daya daga cikin mutanen da suka sauya makomar duniya.Ya jagoranci bil adama daga duhu ya zuwa haske na hakika, daga kasa ya zuwa sararin samaniya.Shi yasa kamata yayi a yaba masa.Ya haramta zubar da jini wadanda ba su ji ba basu gani ba, ya bude kofofin cigaba da yalwa ga duniya.Babu wanda ya taba yin irin wannan abun gabanin sa, kuma bana zaton a bayansa wani zai aikata hakan.Girmamawa,martaba da daukaka su tabbata a gare shi".

5.Thomas Carlyle: Babban marubuci,kwararren a fannin tarihi na kasar Scotland ,wanda aka haifa a 4 ga watan Disamban shekarar 1795 a Ecclefechan,kana ya kwanta dama a ranar  5 ga watan fabarirun shekarar1881 a Landan, ya ce :

"Abin kunya ne ganin yadda kowa ke zargin Musulmai da bin addinin karya.Abin kunya ne ganin yadda kowa ke tuhumar Muhammad da zama manzon karya.Duniya ta shaida cewa a tsawon rayuwarsa, Muhammad ya kasance mutum mai dokoki wadanda ba zasu taba rugujewa ba,farar aniya,kankan da kai,kyauta,tausayi, imani,kamili kana amintacce".

6.Napoléon Bonaparte: Babban sarkin daular Faransa ,wanda aka haifa a ranar  ga watan Agusta shekarar  1769 a Ajaccio,kana ya kwanta dama a ranar 5 ga watan Mayis shekarar 1821 a Longwood, ya ce :

"Islam ya yi watsi da Dagutu.Babu wani abin bauta face Allah, Muhammad kuma manzonsa,wannan kalmar ita ce gimshikin addinin.Muhimmin abinda zamu fahimta a nan shi ne, ya kara tabbatar da kalmar Musa wacce Yesu Al Masihu ya jadadda.Ina fatan wata rana zan yi nasarar hada kanun dukannin masana da ma'ilmantan kasata karkashin inuwar Al Kur'ani".

7.George Bernard Shaw: Babban marubucin kasar Burtaniya , wanda aka haifa a ranar 26 ga watan Yulin shekarar 1856 a Portobello,inda ya kwanta dama a ranar 2 ga watan Nuwamban shekarar 1950, ya ce :

"Abinda duniya ke matukar bukata a yanzu haka, shi ne jagorancin mutum mai tunanin Muhammad.Malaman Kiristan zamanin Middle Age,sabili da jahilici da tsastsaucin ra'ayi,sun dinka shafa wa Muhammad da addininsa bakin fenti.Sun gabatar da Musulunci a msatyin makiyin Kirista.Amma bayan na bincika tarihin wannan mutumin,sai na gano cewar, shi ba makiyin Kirista ba ne, maceci ne na duniya.A ganina inda zai ja akalar mulkin duniyarmu ta yau, da zai warware dukannin matsalolinmu,kana kwanciyar hankali,wadata da farin ciki za su kasance a kowane muhalli da ke doron duniya".

8.Mahatma K. Gandhi: Tsohon shugaban kasar Indiya ,wanda aka haifa a ranar 2 ga watan Oktoban shekarar 1869 a Porbandar,kana ya kwanta dama a ranar 30 ga watan Janairun shekarar 1948 a New Delhi, ya ce :

"Ina bukatar in zurafa sanina game da rayuwar mutumin da ya samu kyaukyawar gurbi a zukatan milyoyin jama'a.Babu makawa na tattaba cewar, ba takobi ne ba yasa Muhammad ya shiga zukatan mabiya addinin Islama.Babu kamar sa a fannin aminci, karamci da daratta na kasa da shi".

 

 

 

 Labarai masu alaka