‘Yan tawaye da sojojin Myammar sun gwabza kazamin rikici

‘Yan tawayen kabila da sojojin Myammar sun gwabza kazamin rikici a jihar Kachin inda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, ya zuwa yanzu an raba sama da mutane dubu 10 da matsugunansu.

Wani jagoran ‘yan tawaye Zau Raw ya bayyana cewa, gwamnatin Myammar na son karar da kabilar Kachin kamar yadda suka yi a Arakan.

Ya ce, wannan abu wani kokari ne na shafar da kabilarsu daga ban kasa.

Zau Raw ya kara da cewa, manufar gwamnati karama ce, kuma suna tsananta rayuwa ga fararen hula da ke yankunan da ake da ‘yan tawaye inda kwnaki na tafiya yara kanana ba sa samun isasshen abinci.

Amma mahukuntan yankin sun ce, ana samun matsalar kai kayan taimako ga fararen hula dubu 120 da aka raba da matsugunansu a Kachin da Shan.Labarai masu alaka