An kai mummunan hari a Amurka

Mutane 3 ne aka tabbatar sun mutu yayinda wasu 3 suka jikkata sakamakon harin da aka kai a jihar Maryland ta Amurka.

An kai mummunan hari a Amurka

Mutane 3 ne aka tabbatar sun mutu yayinda wasu 3 suka jikkata sakamakon harin da aka kai a jihar Maryland ta Amurka.

A harin da aka kai a garin Aberdeen an bude wuta a wajen wata cibiyar raba maguguna.

Shugaban 'yan sandan yankin Harford da ke Maryland ya fitar da sanarwa ta shafinsa na Twitter cewa, suna tabatar da an kai harin a hanyar da ke tsakanin Spesutia da Perryman. An kashe tare da jikkata mutane da yawa.

Wata mace mai shekaru 26 da ba a bayyana sunanta ba ce ta bude wuta a gaban cibiyar raba magungunan.

'Yan sanda sun cimma ta inda ta samu rauni wanda hakan ya janyo mutuwarta a asibiti.

Wani jami'i da ya nemi a boye sunansa ya ce, an kashe mutane 3 a harin.Labarai masu alaka