Bincike: Kaso 28 cikin ɗari na Siriya na hannun 'ƴan ta'adda

Ƙungiyar ta'adda ta YPG/PKK dake Siriya na ci gaba da ha'intar fararen hula a ƙasar.

Bincike: Kaso 28 cikin ɗari na Siriya na hannun 'ƴan ta'adda

Ƙungiyar ta'adda ta YPG/PKK dake Siriya na ci gaba da ha'intar fararen hula a ƙasar.

An karbo bayanai daga mazauna yankin Aynularab a jihar dake tabbatar da kungiyar ta'addar YPG/PKK ta hana shiga da fita a ƙauyuka goma dake yankin.

A yayinda suka hana shiga da fita a yankin El-Kubbe ƴan ta'addar YPG/PKK na ta rangadi akan titunan garin.

Bugu da kari sun kame mata uku da matasa 23 a cikin kwanaki biyu, an dai bayyana cewar an sako fararen hulan a yau.

A yankin da larabawa ke da yawa yan ta'addar sun dinga takurawa fararen hula tare da kwace wayoyin hannu, zinari da sauran kayyayakin fararen hula.

El Kubbe na daya daga cikin yankunan da Larabawa ke ƙalubalantar mamayar yan ta'adda.

Binciken da kanfanin dillancin labaran Anadolu ta yi ya nuna cewar kusan kashi 28 cikin ɗarin ƙasar Siriya na larkaskar mamayar yan ta'addar YPG/PKK.Labarai masu alaka