Hoton Hitler da Bayahudiya Rosa

Duniya na ci gaba da cincirindo don zuwa Amurka da nufin sayen hoto daya tak da tsohon shugaban akidar Nazin kasar Jamus,Hitler ya taba dauka da wani mabiyin addinin Yahudu.

Hoton Hitler da Bayahudiya Rosa

Duniya na ci gaba da cincirindo don zuwa Amurka da nufin sayen hoto daya tak da tsohon shugaban akidar Nazin kasar Jamus,Hitler ya taba dauka da wani mabiyin addinin Yahudu.

Kamar yadda kafar yada labarai ta kasar Burtaniya BBC ta rawaito,an nuna hoton Hitler,wanda ya yi wa sama da Yahudawa milyan 6 kisan kiyashi,da wata Bahudiyar yarinya mai suna Rosa, a Amurka.

A yanzu haka ana ci gaba da gwanjon hoton a gidan nuna kayayyakin tarihi na Alexander da ke jihar Maryland.

Ana kyautata cewa,za a siyar da hoton wanda Heinrich Hoffman ne ya dauki shi,a akalla dalar Amurka dubu 10,000.

Da yake bayani a shafukan intanet shugaban gidan tarihin Alexander,Bill Panagopulos ya ce:"Wannan hoto ne da aka dauka don yada farfaganda.Amma abinda ya fi daukar hankalin jama'a shi ne yadda Hitler ya nuna kusanci ga yarinyar.Na yi matukar mamaki a lokacin da ga hoton.Hitler ya gana da Rosa sabili ranar haifuwarsa ta zo daya da tata".

 

 Labarai masu alaka