Yananyin tattalin arzikin duniya a yau

Ana anfani da tsari maisuna kebabbancen asusu a kusan ko wacce kasa.

Yananyin tattalin arzikin duniya a yau

Asusun yana tallafawa wajen habakar tattalun arzuki da wajen kafa hannun jari, mussaman a kasashen da basu da bukatar kashe dukiya sosai. 

Ana iya kasa asusun zuwa rashe biyu. Wato rashen daya kunshi kasahen da suke cikin kungiyar EMIA da kuma rashen kasashen da basa cikin kungiyar EMIA.

Rashen EMIA dai shi ne Reshen da suke samun arzukinsu ta hanyar sayar da ma’adanan karkeshen kasa kamar su fetur da gas.

Reshen kasashen da basa cikin kungiyar EMIA kuma suna iya aiki kamar sauya kudi, sannan da sarrafa ribar da tayi yawa akan dukiyar kasa.

Norway, Saudi Arabiyya, Kuwet, Dubai, Katar da Rasha sune suka fi ko wacce kasa anfani da Asunsun EMIA.

Asusun hannun jarin kasar Norway yafi na ko wacce kasa inda yake dauke da kimanin  Dolar Amurka miliyan 847.6. Hakan yasa ake anfani da asusun wajen bada hannun jari ga manyan kamfanonin duniya  kamar su Nestle, Royal Dutch Shell, Apple, Roche Holding, Novartis, Alphabet da Microsoft.

Kasar Cana, Singafo da Hong Kong, suna anfani da asusun dukiyar datayi yawa bayan saya da siyarwa tsakanin kasashe. Kuma kasahen na cikin reshen daulolin daba cikin EMIA.

Cana nada arzuki kimanin dolar Amurka 813.8  a matsayinta ta kasa mai asusun da baya cikin kungiyar EMIA. Kuma tana tura dukiyar ne wajen kwangilar da New Silk Road Initiative and Asian Infrastructure Investment Bank suke yi.

Yanzu dai ajandar kugiyar kebabbancen asusun ya hada da habakar tattalin arzuki dakuma samarda kwanciyar hankalin kasa dan karnin gaba su faidancu da shi. Sannan da anfani macroenomic politics wajen Karfafa tatallin arzukin ta inda ba zai rushe ba, da kuma bada taimako wajen cigaban tattalin arzukin.

Fa’idodin kebabban asusun kuwa ana iya ganinsu a wurare da dama.

Musamman a kasashen da sukaci gaba kebabbancun asusan suna taimakawa wajen bada hannun jari. Sannan suna iya taimaka tattalin arzukin kasa yayinda ya gurbata.

A gefe guda, kebabbancun asusan suna jan hankali wajen iya daidaita  kasuwoyi daban daban.

Kebabbancun asusan dai suna kara kima a yau da gobe a kasahen  da suka ci gaba da kuma wanda sukeci gaba. Darajar asusan yakai kimanin dalar Amuraka tiriliyon 7.4.

A halin yanzu yawan asusan yakai kimanin arba’in a kasashe daban daban. Kuma arzukin wadannan asusai ana samunsu ne wajan harkokin tattalin arzuki daga Asiya ta Tsakiya. Sannar ana danganta habakar asusun da cibiyoyin tattalin arzuki na kashen gabas wato Far East.

Za a iya samun asusan a kasashen G-20 gabaki dayansu banda kasar Turkiya. Bayan kammala wasu ayyuka kuwa an bude sabon asusun a kasar Turkiyya a 26. Agusta. 2016.  Attajuran kasar sun dauki nauyin ginin Asusun sannan suka mika jagorancin asusun ga gomnatin kasar.

Kasar Turkiya zata yi anfani da asusun wajan cika burinta kamar haka; hana gurguncewar tattalin arzukin wasu kasahe, bada dokiya domin cigaban ayyukan kimiya da sayan kaya wajen yin ayyuka makamantan haka, cigaban hannun jarin musulunci, taimako wajan habakar tallalin arzuki, da kuma samo ayyuka masu karancin kashe kashe. 

Kasar Turkiyan zata yi anfani da asusun mussanman wajan bada hannun jari ga kamfanin jirgin kasa da kuma taimakawa kamfanunnukan ayyukan fasaha wajan ganin tattalin arzukin kasar yaci gaba. Sannan Asusun zaiyi kokarin ganin tattalin arzukin kasar ya kamo daraja mafi girma a duniya.

A takaice dai anyi asusun EMIA dakuma reshen tsarin dukiyar datayi yawa ne,  domin assasa tattalin arzukin kasa wanda zai dade. Ana anfani da wannan tsarin asusu shekara da shekaru a kasashen da suka ci gaba dakuma kasashen da sai yanzu suke ci gaba.  Anan dai za a iya cewa Kebabbancen asusun Turkiyyan zai taimaka matuka wajan ganin kasar ta cimma burinta.

 

 Labarai masu alaka