Bukatar Sassaukan ra’ayi ga Yammacin Duniya

Matsalar Tsaurin ra'ayi a Kasashen Yamma: Yaya Halayyar Yammacin Duniya ta ke a yau game da yadda suke mu'amala ga bakin mutane a kasashensu?

Bukatar Sassaukan ra’ayi ga Yammacin Duniya

Matsalolin Kasashen Duniya-10

Masu karatu barkanmu dai, tare da sake kasance wa a cikin sabon shirin Matsalolin Kasashen Duniya. Kamar kowanne mako, a wannan makon ma za mu kawo muku sharhin da Farfesa Kudret Bulbul Shugaban Tsangayar Nazarin Harkokin Siyasa na Jami’ar Yildirim Beyazit ya yi mana.

Siyasar tarihi, idan har za a dauki izina daga gare ta, to har iya ina za a iya dauka a matsayin mai bayar da darasi. Amma abin takaici ba a daukar wani darasi ko kadan. Nan da nan ake saurin manta wa da munanan abubuwa, bakin ciki da wahalhalun da aka sha a duniya.

A karnin da ya gabata an yi yake-yake guda 2 da aka zubar da jini, hawaye tare da karkashe mutane ba don komai ba sai kawai saboda bukatar kasashen yamma na su yi mulkin mallaka. Bayan yakin duniya na 1 da na 2 sai Turai ta shiga sabon yanayi na samar da tsarin da za ta tafi a kai. An samar da Tarayyar Turai wadda ta samar da ‘yanci, walwala, demokradiyya da zaman lafiya ga Turai baki daya.

Daga Turai mai saukin ra’ayi zuwa mai tsattsaura

Amma matakin da muka kawo a yau ya zama na barazana ga duniya. Sanarwar da Amurka, Koriya ta Arewa da Rasha suka fitar a baya-bayan nan abin ya zama kamar za su farwa juna tare da fara yakin Nukiliyata yadda za a ga makamin waye ya fi karfi, waye zai fara dannan madannin makamin.

Hakkokin dan adam a Turai, ‘yanci, yawaitar al’umu, ‘Yancin Addini, bin tsarin rayuwa na daban na kara tabarbarewa a kowacce rana a Turai. Kyamar Musulunci da ‘yan gudun hijira na kara yawa a koyaushe. Alkaluman Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Jamus na nuna cewa, a shekarar 2017 an kai wa Musulmai hari sau 950 a kasar. Za ku iya samun cikakken rahoton shafin yanar gizo kamar haka: www.spiegel.de. Da a ce a wata kasar Musulmi da ke Latin Amurka ko a Gabashin Duniya za a kaiwa Kirista ko Yahudu hari sau daya bisa dari na wadannan hare-hare 950, to ba za mu iya hasashen mattani da duniya za ta mayar ba. Babu shakku, ba za a taba fatan afkuwar wannan abu ba. Shirme da hare-haren da suke afkuwa a Turai bai kamata su zama misali ga wani bangare na duniya ba. Hari kan Musulmi a Turai ba a kasar jamus kawai ya tsaya ba. Idan abin ya faru a Turai sai a yi shiru. Mutanen da suke da tsarin rayuwa na daban a Maurka da Turai ba su ji irin wannan abu da ake yi musu ba.

A lokacin da kasashen Turai da dama suke hana mutanen da aka zalunta, marayu da masu neman mafaka gurin zama, sai ga shisuna ba w ‘yan ta’adda irin su FETÖ, PKK, DHKPC da sauransu. Suna bayar da mafaka ga mutanen da suka aikata ta’addanci a kasashensu kai kusan ma gayyatar su suke yi. Shin akwai wata kasa a duniya da ta ke ba wa ‘yan ta’adda mafaka sama da kasashen Turai? Anya kuwa a kwai?. Ina mamaki.

A gefe guda, masu ranjin ‘yanci, kare hakkokin dan adam, demokradiyya da yawaitar jama’a na kara durkushe wa. A yanzu ba jam’iyyun fafutukar ‘yanci ko na demokradiyya ne suke nasarar zabe ba, a a na nuna wariya, nuna bambanci da ra’ayin Nazi ne suke yin nasara. A yanzu babu tunani mai kyau a Turai, nahiyar ta zama ta shugabanni masu barazana ga makotansa da kasashen da ke kewaye da su.

Mummunar Yamma ko karshen tarihi

Ku yi tunanin a ce karshen dan adam zai zo ta hanyar harba makaman Nukiliya da masu guba da kasashen yamma suke da su. Ta yaya ake amfani da wadannan makamai da ke hannun wadanda suke nuna kyama, bambanci, wariya, tsana sda zalunci mamakon so da kauna, ‘yanci da kare hakkokin dan adam? Ko a mafarki wannan abun tsoro ne. Na razana dan adam. Duk da cewa a lokacin yakin duniya na farko da na biyu wadannan makamai ba su da barazana kamar yau amma ku kalli irin barnar da suka yi. Idan aka yi tunani kan makaman kare dangi a yau, to yadda makaman suke shiga hannun masu tsurin ra’ayi watakila gayyatar Kiyama ce. A yanzu wasu ‘yan gode da nşisa sun fara rubutu kan “Ana karbar Alkiyama daga Hannun Ubangiji” ko kuma “Ana takurawa Ubangiji ya tashi Alkiyama”.

A kasashen da ake nuna wariya, aka tafiyar da hakkokin dan adam, ‘yanci da dadin rayuwa da darajojin duniya, shin wannan “barazana” shin za su zauna kalau? Tarihi ba ya fadin haka. Bayan kisan kare dangi na Yahudawa. An ga yadda mutane suka ci gaba da sanyawa yankunansu wuta.

Bukatar Sassaukan ra’ayi ga Yammacin Duniya

Yadda lamarin barazanar da Turai ke yi ke kara kusantowa, to Yammacin duniyar na ganin ba shi da bukatar “Sassaukan Ra’ayi” Amma yana muhawara kan “Musulunci Mai Sauki”. Musulunci Sassauka wani batun rubutu ne na daban. Idan haka ne lamurkan tsaurara ra’ayi na da ban tsoro ga kowa. Yadda masu kyakkyawan hali masu kare hakkoki da ‘Yancin dan adam, masu dabbaka demkoradiyya suke fadu wa zabe a Turai, ba iya makomar nahiyar Turai zai cutar ba. Mun ga yadda masu rajin sauyi cikin gaggawa suka jefa Turai a karnin da ya gabata. A saboda haka dole ne masu rajin ‘yanci da son zaman lafiya su yi aiki tare da Turai don samar da zaman lafiya a doron kasa.

Sharhin da Farfesa Kudret Bulbul Shugaban Tsangayar Nazarin Harkokin Kasa da Kasa na Jami’ar Yildirim Beyazit ya yi mana.Labarai masu alaka