Samfuran jiragen sama marasa matuka na kasar Turkiyya

Muna gabatar muku da sharhin Tarkan Zengin, shugaban horo na kungiyar kwadago ta masana’antar kera makaman yaki ta Turkiyya.

Samfuran jiragen sama marasa matuka na kasar Turkiyya

Samfuran jirage marasa matuka masu dankare da makamai da kuma marasa su da masana’antun tsaron Turkiyya suka kera, sun sa kasar ta kasance a sahun manyan kasashen duniya.

Yayin da a daya bangare take ci gaba da kera makamai masu matukar muhimmanci a fagen tsaro, a daya gefen kuma, Turkiyya ta cim ma gaggarumin matsayi da kuma daga martabarta a idon duniya, a goggayar da take ci gaba yi da sauran kasashe takwarorinta ta hanyar tanadar ingantattun hanyoyin tabbatar tsaro,wadanda ta samar da karan kanta.Tare da aiyukan da ta yi a wannan fannin, Turkiyya ta samar da siyasoshin dogaro da kai,kana a sanadin makaman da sayar wa kasashen ketare, tattalin arzikinta ya bunkasa matuka gaya.Ko da yake daman,gwagwarmayar da kasar ke ci gaba da yi na kera jiragen sama marasa matuka, ba komai ba ne, fa ce yunkurin kara tabbatar da ‘yancin kai da kuma habbaka tattalin arziki.Jirage marasa matuka na farko da rundunar sojan kasar Turkiyya ta fara mallaka a shekarar 1990,su ne HERON kirar kasar Isra’ila da kuma GNAT,kirar Amurka.A shekarar 2000, Turkiyya ta yi kokarin sayen sabbin samfuran jiragen GNAT, wato jirage marasa matuka  Predator da Repaer, amma ‘yan majalisar dattijan Amurka ta hau doki naki.Wannan shi ne dalilin yasa Turkiyya ta daura damarar kera jiragen na saman marasa matuka da kashin kanta.A yau, kasar na yin amfani da ire-iren wadannan na’urorin yaki samfarin Anka da Bayraktar,wadanda ita ce ta kera su.

Sakamakon kera jiragen sama marasa matuka masu dankare da makamai (SİHA) da kuma marasa su (İHA),Turkiyya ta shiga sahun manyan kasashen duniya masu fada a ji.A yau, kasar ta mallaki gaggarumin karfi mai tasiri kwarai da gaske.Kowa ya shaida ababen mu’jiza da matasanta ke iya yi,idan har an ba su dama.Tsaro, haka ce da za ta iya cim ma ruwa,idan har an sa manufofin dogon zamani a gaba, kana aka dinka fafutukar cim musu cikin hakuri.A yau fara kera jiragen sama marasa matuka masu dankare da makamai (SİHA) da marasa su (İHA) da Turkiyya ta yi a wadannan ‘yan shekaru 10,sakamako ne na tsawon lokacin da kasar ta dauka tana gwagwarmayar cim ma manufofin da ta kafa.

Da ya ke tsokaci game da jiragen sama marasa matuka,daya daga cikin kusoshin kamfanin Baykar,wacce ta taka rawar a zo a gani wajen kera wadannan makaman yakin a Turkiyya,Selçuk Bayraktar ya ce :

“Tarihin wadannan makaman ya fare  da na kananan jiragen sama marasa matuka.Bayan wannan nasarar, sai muka yanke shawarar hada karfi da karfe da sojoji a sansanonin da jirage ke shawagi, don ci ma mataki na gaba.Kananan jiragen sama marasa matuka sun tanadi fasalolin daukar hotuna kai-tsaye da kuma hada su don zana taswira.Wannan abu ne da babu wani jirgin sama marar matukin da yake da shi.An cim ma wannan matakin, bayan gaggarumar kwarewa da cigaba da aka samu a gwgwarmayar tabbatar da tsaro a yankin Afrin na kasar Sham.A shekarar da ta gabata ma, jiragen sun ci karo da lamurran da suka sha bamban da wadanda suba ma fuskanta a farmakon tsaro na Firat”.

KANANA DA TSARARRUN JİRAGEN SAMA MARASA MATUKA SAMFARİN BAYRAKTAR

Na’urorin yaki kirar Turkiyya na farko da rundunar sojan kasar ta fara amfani da su a shekarar 2007, su ne kanana jiragen sama marasa matuka wadanda kamfanin Bayraktar ta samar.

Kamfanin wanda ta bisani ta kera tsararrun jiragen sama marasa matuka, ta gabatar da fasalolin hajojinta kamar haka:Samfarin karamin jirgin sama marar matuki na Bayraktar, wata na’urar yaki mai lantarki da aka kera Turkiyya,kana tare da masaraffinta na zahiri da na badini, ta kasance mutum-mutumi mafi kankanci da ke shawagi a sararin samaniya.Tun lokacin da aka kera shi ya zuwa yau,jirgin ya keta hazo sau akalla dubu 100,000.

Na’ura ce da ake yi amfani da ita ko a matsanancin yanayin sararin samaniya da kasa.Tsararren jirgin sama marar matuki kuma, an kera shi ne da cim ma manufofin da ke dogo ko kuma matsakaicin tazara.Na’urar na iya sarrafa kanta ta hanyar tashi,sauka,leko sirruka,shawagi da komawa indi ta fito lami-lafiya.Tare da tsare-tsarensa uku na sa ido kan tashi da sauka,samfuran manhajojinsa na sarrafa shawagi da kuma maganadisansa masu hangen nesa,tsararren jirgin sama marar matuki na kamfanin Bayraktar ya kasance, wata ingatacciyar na’urar bincike da leken asiri wacce ke da muhimmin matsayi a jerin nagartatun na’urarori masu karko na wannan zamanin da muke ciki.Jirgin ya yi tashinsa na farko a watannin Satumba da na Oktoban shekarar 2009 a gaban shugabannin kasar Turkiyya.

TASİRİN JİRAGEN SAMA MARASA MATUKA A FARMAKAN TSARO

Jiragen sama marasa matuka masu dankare da makamai (SİHA) da kuma marasa su (İHA), sun taimaka sosai wajen cim ma gaggaruman nasarori a farmakan kawar da kungiyoyin ta’adda da Turkiyya da ta kaddamar a ciki da wajen kasar.Tun a shekarar 2015 kawo yanzu, ake ci gaba da amfani da ire-iren wadannan na’urorin yaki ,samfurin TB2 Bayraktar Jiragen TB2 na cika aiki ba tare an gansu ko kuma an ji kararsu ba,inda suke daukar hotuna masu cikakkun bayanai a tazara mai nesan gaske a sararin samaniya.Musamman ma a farmakan tssaro na Firat da Reshen Zaitun,inda suka taimaka sosai wajen binciko,gano da kuma yin luguden wuta kan ‘yan ta’adda.A hare-haren reshen Zaitun,an kauda yawancin barazanonin da ke kan hanyar sojoji da kuma gano kogunan duwatsu da hanyoyin karkashin kasar da ‘yan ta’adda ke boye a ciki tare da halaka ‘yan harmtattun kungiyoyin, ta hanyar amfani da wadannan jiragen saman marasa matuka.

A yanzu haka ana ci gaba da samar wasu sabbin fasashohin kara inganta wadannan jiragen.Kamfanin Baykar da kawayenta sun samar da manhajar KUZGUN,wacce ke aika hotunan da jiragen sama marasa matuka suka dauka, kai-tsaye  kan na’urorin masu kwalkwawa na sojoji, a duk inda suka.An fara amfani da ita a garo na atiasayen sojojin Turkiyya da na kawayenta, wanda aka gudanar a yankin Efes na kasar, a shekarar 2018.Tare da wannan sabuwar manhajar, sojojin Turkiyya na iya bin diddigin illahirin kungiyoyin ta’addar suka kafu a  ciki ko a gaf da iyakokinta sau da kafa.

Abinsa yasa jami’an tsaron kasar ke iya amfani da hotunan da suke samu a kai a kai don yin babbar galaba a gwagwarmayarsu ta kawat kungiyoyin ta’adda.Bayan ta yi muhimmiyar nasara a fannin kera jiragen sama marasa matuka, a yanzu,manufar Turkiyya ita ce,samar da jiragen sama na kawa marasa matuka.Hakar kasar,wacce cikin kankanin lokaci ta yi nasarar kera wadannan na’urorin yakin, na iya cim ma ruwa.Labarai masu alaka