Odinga ya ce ba zai shiga zaben shugaban kasar Kenya da za a sake yi ba

Shugaban 'yan adawar Kenya Reila Odinga ya bayyana cewa, ba zai shiga zaben shugaban kasar Kenya da za a sake gudanarwa a ranar 26 ga watan nan na Oktoba ba saboda ya fahimci zai zama mummuna sama da na farko.

Wannan mataki na Odinga ya zo ne kwanaki kadan kafin a gudanar da zaben.

A taron manema labarai da ya kira ya bayyana cewa, ya janye daga shiga zaben ne saboda a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

A ranar 1 ga watan Satumba ne kotun kolin Kenya ta rushe zaben da aka gudanar na shugaban kasa wanda aka sanar da shugaba Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya yi nasara.

Kotun dai ta ce, ba a bi ka'idojin da suka kamata ba a yayin gudanar da zaben wanda hakan ya sanya ta nemi da a gudanar da sabon zabe.

A wata sanarwa da Hukumar Zaben Kenyan ta fitar an rawaito shugabar Hukumar Wafula Chebukati na cewa, sun shirya tsaf don gudanar da sabon zabe da ya dace da dokokin da kotun kolin kasar ta fitar. Kuma za a gudanar da zaben a ranar 26 ga watan Oktoba.Labarai masu alaka