• Bidiyo

Kama shugaban 'yan awaren Kamaru ba zai kawo karshen rikicin kasar ba

Wani kwararre kan warware rikicin siyasa Faith Mabera ya sanar da kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa, kama shugaban 'yan awaren Kamaru Julius Sisiku Ayuk Tabe ba zai kawo karshen rikici da zanga-zangar da ake yi ba.

Mai fautukar ya bayyana cewa, a makon da ya gabata ne aka kama shugaban 'yan awaren Julius Sisiku Ayuk Tabe tare da wasu mataimakansa su 10 a Abuja babban birnin Najeriya.

An kama Tabe bisa zarginsa da hannu a yin kulla-kullar raba kasar Kamaru.

A watan Disamba hukumomin Najeriya sun bayyana cewa, ba sa goyon bayan msu neman raba kasar Kamaru da suka fito daga yankin da ake magana da yaren Ingilishi.

Mabera ya kuma shaida cewa, kama shugaban 'yan awaren zai sake rura wutar rikicin ne kawai.Labarai masu alaka