Jamus ta bayyana damuwarta kan yadda Isra'ila ke mamayar yankunan Falasdinawa

Ma'aikatar Harkokin Wajen Jamus ta bayyana cewa, akwai damuwa kan yadda Isra'ila ke ci gaba da mamayar yankunan Falasdinawa ta hanyar yin sabbin gine-gine.

Sanarwar da Ma'aikatar ta fitar ta ce, yadda Yahudawa ke mamaye yankunan Falasdinawa da a shekarar 1967 aka amince da nasu ne, da yadda Isra'ila ke gina ofisoshin 'yan sanda a gonakin Falasdinawa abu ne da sanya damuwa sosai.

Sanarwar ta bukaci dukkan bangarorin 2 da su nutsu tare da tattauna hanyar neman mafita da zaman lafiya mai dore wa.Labarai masu alaka