Jiragen yakin Rasha da Ingila sun harari juna a sararin samaniya

Jiragen saman Ingila na yaki sun yi tashin gargadi ga jiragen Rasha da suka yi yunkurin shiga sararin samaniyar kasarsu.

Jiragen yakin Rasha da Ingila sun harari juna a sararin samaniya

Jiragen saman Ingila na yaki sun yi tashin gargadi ga jiragen Rasha da suka yi yunkurin shiga sararin samaniyar kasarsu.

Sanarwar da ma'aikatar tsaro ta Ingila ta fitar ta ce, jiragen yakin Rasha 2 samfurin Tupolev TU 160 sun kusanci sararin samaniyar Ingila inda nan da nan jiragen RAF Tayfun suka tashi tare da hana su shiga yankin na Ingila.

Sanarwar ta ce, lamarin ya faru a ranar Litinin din nan a kusa da iyakar Scotland.

A lokuta da dama a baya ma jiragen yakin Rasha sun yi kokarin shiga sararin samaniyar Ingila inda sojojn saman kasar suke mayar musu da martani.Labarai masu alaka