Turkiyya ta mayar wa da Amurka martani kan abin kunyar da ta yi

Turkiyya ta mayar wa da Amurka martani kan hukunci mai ban kunya da Amurkan ta dauka na ci gaba da taimaka wa 'yan ta'adda a kasar Siriya.

Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar ta ce, ba za a amince da yadda Amurka ke taimaka wa 'yan ta'addar ypg ba wanda hakan ke barazana ga tsaron Turkiyya tare da jefa Siriya yanyi mawuyaci.

Sanarwar ta ce, Turkiyya na la'antar wannan hali na Amurka wanda ta ki ta daina, kuma Turkiyya ta dauki matakin yakar duk wata barazana da za a yi mata, haka nan ya kamara a tuna da cewa, kasar na da ikon yin hakan.

Shi ma kakakin Fadar Shugaban Kasar Turkiyya Ibrahim Kalin ya ce, ba za a amince da wannan mummunan hali na Amurka ba. Dole ne Amurka ta canja daga wannan abun kunya da ta ke yi.Labarai masu alaka