Yadda alakar Turkiyya da Ozbekistan ta sauya sabon salo

Jama'a barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin manufar Turkiyya a kasashen Ketare.Shekara daya kenan da shugaban kasar Ozbekistan, Şevket Mirziyayev ya hau kan karagar mulki.

Yadda alakar Turkiyya da Ozbekistan ta sauya sabon salo

Shi yasa a wannan mako, muka yanke shawarar yin nazari kan huldar Turkiyya da Ozbekistan.

Za mu gabatar muku da sharhin Dokta Cemil Doğaç, na tsangayar harkokin duniya ta jam’iyyar Atatürk da ke Türkiyya.

Şevket Mirziyayev ya fara jan akalar mulkin Ozbekistan,sakamakon lashe zaben shugaban kasa da ya yi, tun bayan Islam Kerimov wanda ya share shekaru 25 kan karagar mulki ya kwanta dama.Shekara daya cif kenan da Şevket Mirziyayev ya zama shugaban kasar Ozbekistan,inda a watan Fabrairun bara, ya fitar da sabbin tsare-tsare a fannonin daban-daban tare da rattaba hannu a kudurin bunkasa cigaban kasarsa na shekarar 2017-2021.Cigaba mafi muhimmanci da duniya ta shaida a Ozbekistan a wannan shekara 1,shi ne habbakar tattalin arzikin da kasar ta samu.A cikin wannan matsakaicin zamani, Mirziyayev ya dora tattalin arzikin kasarsa wanda ya durkushe sakamakon guragun tsare-tsaren gwamnatin baya,kan kyaukyawar turba,ta hanyar kawo kusan gyare-gyare 40 wadanda ke nasaba da 'yancin kasuwanci.Ga dukannin alamu,sabon shugaban Ozbekistan yayi watsi da siyasar magabacinsa Kerimov, wanda ya rungumi tsarin kadaici.Saboda yana ci gaba da nuna kaimi a wajen daidaita huldar da ke tsakanin kasarsa da sauran kasashen Turkawa.Yin ziyararsa ta tarko a kasar Turkmenistan,wata babbar alama ce na kyaukyawan burin da ya sa gaba.A watannin 14 da suka shude,Mirziyayev ya ware dukannin lokacinsa a wajen gana wa da shugabannin kasashen Turkawa.Shugaban na Ozbekistan, ya gana da takwaransa na Kazakistan sau 6,na Turkmenistan da Kirgizistan kuma, sau 3.

Bugu da kari, ya gana da shugaba Erdoğan sau 2 ta hanyar kawo ziyara Turkiyya sau daya, inda shugaban na Turkiyya kuma ya ziyarci Ozbekistan sau 1.Wannan wata babbar dama ce ga kasar Ozbekistan a yunkurinta na karfafa dangantakar da ke tsakanin ta da makwabtanta da kuma hada kansu tamkar tsintsiya madaurinki daya.Tsakanin ranakun 10 da 11 na watan Nuwamban shekarar 2017, a karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya, an gudanar da wani babban taro mai taken "Tsaro da dauwamammen cigaba a Asiya ta Tsakiya" a birnin Semerkand na kasar Ozbekistan.A wannan taron, shugabannin kasashen Asiya ta Tsakiya sun yanke shawarar ganawa a albarkacin bikin murnar karshen bazara na Newruz na shekarar 2018.Wannan fadada hadin gwiwa tsakanin jamhuriyoyin kasashen Turkawa, zata iya zama wata cancantacciyar hujja a wajen tabo batun 'yantacciyar kasar Turkistan mai cin gashin kanta.Nan da wani matsakaicin lokaci,Ozbekistan wacce ke gaf da sauran kasashen 4 na yankin Asiya ta Tsakiya, na iya zama cibiyar kasuwancin wannan yankin.

A shekara ta farko,Mirziyayev ya fafada 'yancin fadar bakin kafafan yada labarai. Ya dauki kwararan matakai a wajen 'yantar da 'yan kasarsa daga tilashin yin noma.Daga ranar 1 na watan Janairun shekarar 2019,gwamnatin Ozbekistan ta yanke shawarar dage dokokin hana wa al'umar kasar bizar fita kasashen waje ba izininta ba. Bugu da kari,daga ranar 10 ga watan Fabrairun bana,za a fara bai wa 'yan kasar Turkiyya damar share kwanaki 30 a Ozbekistan ba tare da sun karbi biza ba.Babu makawa, wannan wani babban cigaba ne. A shekarar 1991,Turkiyya ce kasar da ta fara yin na'am da cin gashin kan kasar Ozbekistan.Shi yasa huldar da ke tsakanin kasashen 2 ya habbaka haikan.Dangane da batun harin ta'addanci na yankin Andican,wanda aka tattauna a zauren Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 2005,Turkiyya ta mara wa Ozbekistan baya.Abinda yasa wannan alakar da ta fara tun a shekarar 1991, ta ci gaba da bunkasa har ya zuwa shekarar 2005.Amma, ziyarce-ziyarce da shugaba Erdoğan da takwaransa Mirziyayev suka dinka yi wa juna, ya kara karfafa huldar da ke tsakanin su.A ganawar da suka yi a Semerkand, shugaba Erdoğan ya ce :" Mun buda sabon shafi a littafin huldar da ke tsaninmu" a yayin da Mirziyayev kuma ya ce :"Daga yau cacar baki ta zo karshe,yanzu lokaci ne na kulla tantagaryar hulda".Idan muka yi la'akari da yadda harkoki ke ci gaba da wakana a kasashen 2, zamu gane irin babbar ma'anar da wadannan bayanan ke da ita a yau.Ozbekistan kasa ce da ta karkarta akalar zuciyar ya zuwa Turkiyya,sabili da dangantakar tarihi da ke tsakanin su.Halin ko-in-kula da kasashen 2 suka dinka yi wa juna tsawon lokaci mai tsawon gaske ya zo karshe,inda a yanzu suka hada karfi da karfe don yakar ta'addanci da kuma inganta kiwon lafiya,yawon bude ido,kasuwancin yaduka da na fatu.Haka zalika, kamata yayi wannan hadinkan ya amfanar da fararen hula,kafafan yada labarai da ilimi.Samar da cibiyar ilimi kamar jami'ar "Hada kan Turkiyya da Kazakistan Ahmet Yesevi" da ke Kazakistan, na iya taimakawa sosai. Gina tagwayen jami'o'i na "Hadan Turkiyya da Ozbekistan na Uluğ Bey" a Santambul da Semerkand, zasu taimaka matuka gaya a wajen samar da rumbun sani game da tarihin Turkawa da kuma bunkasa harshen Turkanci.Yin amfani da akidar sufi ta Hanefi-Matudiri gadon kasashen 2, a matsayin katangar karfen da zai yi wa tunanin Salafiyanci katsa landan a yankin Eurasia,wata madaidaiciyar hanya ce.Shi yasa ya ci a ce, kasashen 2 sun zage damtse,don akwai aiki tukuru a gabansu.Mirziyayev ya bude sabon shafi a tarihin kasarsa.Marigayi Kerimov, ya kasance mai taka tsantsan da kuma nesanta kansa da duk wata siyasar da ta shafi yankin Turkawa.Wannan sauyin numfashin,wata gaggarumar nasara ce ga masu fada a ji na yankin Eurasia da kuma Ozbekistan.Kowa ya san da cewa, kasar na fama da mishkilolin da suka jibanci karancin kudi da kuma makamashi.Ana iya magance wadannan matsalolin ta hanyar gayyatar masu zuba jari na kasashen waje da na kungiyar hadinkan kasashen Turkuwa zuwa Ozbekistan.Mirziyayev yana da cikakkiyar masaniya game da kasa da kuma yankinsa, kana ya kware haikan a wannan fannin.A 'yan kwanaki masu zuwa, habbaka alakokin Ozbekistan da kungiyar hadinkan kasashen Turkawa, na da matukar muhimmanci a yankin Eurasia da ma duniyar Turkawaga baki dayanta.Domin Ozbekistan cibiya ce ta duniyar Turkawa.

Mun gabatar muku da sharhin Dokta Cemil Doğaç na tsangayar harkokin duniya ta jam’iyyar Atatürk da ke Türkiyya.Labarai masu alaka