Amurka da Saudiyya sun fara atisayen soji mai taken "Kawancen 2018"

Dakarun Sojin Amurka da na Saudiyya sun fara gudanar da wani atisaye mai taken "Kawancen 2018".

Amurka da Saudiyya sun fara atisayen soji mai taken "Kawancen 2018"

Dakarun Sojin Amurka da na Saudiyya sun fara gudanar da wani atisaye mai taken "Kawancen 2018".

A ranar Lahadin nan aka fara atisayen a arewacin Saudiyya inda za a daukimako guda ana gudanarwa.

Manufar atisayen karo na 4 da kasashen suke gudanarwa shi ne a sake karfafa alakar soji, hadin kai da samar da tsare-tsare da za su taimaki kasashen na Amurka da Saudiyya.

Haka zalika atisayen na hadin gwiwa na da manufar koyar da wasu hanyoyin yaki na musamman da ba a saba ganinsu ba.

Kwamandan Dakarun Saudiyya da ke Arewacin Kasar Manjo Janar Salih Al-Zahrani ya bayyana cewa, sojojin da ke halartar atisayen za su sake samun karin kwarewar yaki tare da iya amfanin da manyan makamai na zamani.Labarai masu alaka