• Bidiyo

Tarayyar Larabawa ta ayyana Kudus a matsayin Birninta na Gado

Kungiyar Tarayyar Larabawa ta ayyana Kudus a matsayin Birninta na Gado kuma na dindidin.

Tarayyar Larabawa ta ayyana Kudus a matsayin Birninta na Gado

Kungiyar Tarayyar Larabawa ta ayyana Kudus a matsayin Birninta na Gado kuma na dindidin.

Kamfanin dillancin labarai na Falasdin WAFA ya bayar da labarin cewa, Kasashe Mambobin Tarayyar sun gudanar da wani biki a hwlkwatar Kungiyar da ke birnin Alkahira na Masar sakamakon ranar ta Birnin Kudus.

Shugaban Kungiyar Raya Kudus Halil Karraje Al-Rufa'i ne ya jagoranci zaman inda a jawabin da ya yi ya ce, Tarayyar Larabawa ta amince da Kudus ya zama Birninta na Gado kuma a shekarar 2019 za a gudanar da babban bikin tuna wannan rana.

A watannin baya ne dai shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ayyana Kudus a matsayin helkwatar Isra'ila wanda hakan ya janyo hayaniya a duniya baki daya.Labarai masu alaka