Japan ta gargadi Koriya ta Arewa

Firaministan kasar Japan Shinzo Abe ya yi kira ga kasar Koriya ta Arewa da ta dauki matakan da suka dace wajen warware matsaloli  makaman nukiliya da kasar ke fama dashi.

Kamar yadda kanfanin dillancin labaren Kyodo ta sanar Firaminista Abe kafin ganarwarsa da shugaban hukumar leken asirin kasar Koriya ta Kudu Suh Hoon ya bayyana cewar tattaunawa akan kauda makaman nukiliya na samun tagomashi.

A yayinda da ya ce: "Ya kamata Koriya ta Arewa ta dauki matakan kauda makaman nukiliya, domin hakan nada muhinmanci." 

Bayan ganawar Suh da Abe, an bayyana cewar kauda makaman nukiliya zai inganta dangantakar dake tsakanin Koriya ta Arewa da ta Kudu.

Suh, ya bayyana cewar ganawar da Koriya ta Arewa da ta Kudu da kuma Amurka zasu yi nada muhinmanci sosai.

A dayan barayin kuma firaministan Japan Abe zai ziyarci Amurka a watan gobe.

 Labarai masu alaka