Iran ta zargi Amurka da yunkurin raba Kasashen Gabas ta Tsakiya

Ministan Tsaron Iran Emir Hatemi ya bayyana cewa, Amurka na ta kokarin ganin ta raba wasu Kasashen Gabas ta Tsakiya ta hanyar amfani da gwamnatin arewacin Iraki mai cin gashin kanta amma ta hanyar taimakon Iran, Turkiyya da Iraki ba za ta yi nasara ba.

Iran ta zargi Amurka da yunkurin raba Kasashen Gabas ta Tsakiya

Ministan Tsaron Iran Emir Hatemi ya bayyana cewa, Amurka na ta kokarin ganin ta raba wasu Kasashen Gabas ta Tsakiya ta hanyar amfani da gwamnatin arewacin Iraki mai cin gashin kanta amma ta hanyar taimakon Iran, Turkiyya da Iraki Amurkan ba za ta yi nasara ba.

Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya rawaito Hatemi na magana a wajen taron Taswirar Iran karo na 13 da aka shirya a Birnin Tehran inda ya zargi Amurka da aiyukan lalata kan iyakokin Kasashen Gabas ta Tsakiya.

Ya ce, Makiya sun fara yaudarar gwamnatin arewacin Iraki mai cin gashin kanta tare da yunkurin raba Kasashen yankin, amma bayan farkawar mutane tare da taimakon Iran, Turkiyya da Iraki ba su yi nasara ba.

Hatemi ya ci gaba da cewa, manufar Amurka a Gabas ta Stakiya ita ce tabbatar da wannan abu.

 Labarai masu alaka